Duniyar Sadarwa

Sababbin al'amuran fasahar sadarwan zamani, shawarwari da bayanan yadda ake... a harshen Hausa!

WhatsApp zai fito da tsarin samun taska daya a wayoyi daban

Wallafan October 10, 2020. 3:23pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Labaran Fasaha

Manhajar WhatsApp na yunkurin fito da wani sabon tsari da zai bai wa masu amfani da shi daman samun taska daya a kan wayoyi daban-daban wato 'one account, multiple device' a turance. Tsari ne da zai ba mutum daman yin rajistan WhatsApp tare da lamban waya guda daya amma a kan wayoyi fiye da daya. Wato ba kaman yadda tsarin ya ke a yanzu ba, wanda ke bai wa mutum daman yin rajista da lamban waya guda daya a kan waya daya kawai.

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/10/1/whasapp_08-w810h462.jpg_thump.jpg

Wani kamfanin labaran WhatsApp mai suna BETAinfo ya ruwaito cewan wannan sabon tsarin zai bai wa masu amfani da WhatsApp din daman yin rajista da lamba daya a kan wayoyi har guda hudu. Sai dai rahoton ya bayyana cewan har yanzu ana can ana kan yin gwaji ne na wannan sabon tsari, kuma ba a riga an sake shi domin al'umma su fara nasu gwajin ba.

Ana ganin wannan sabon tsarin zai kasance abu na biyu da zai kayatar da masu amfani da manhajar na WhatsApp a wannan shekara ta 2020. Baya ga sabon tsarin gayyatar abokin hira ta hanyar 'QR code' da manhajar ya fito da shi a watan Mayun da ta gabata. Kuma fitowan wannan tsari zai kara ba WhatsApp din daman yin gogayya da takwarar sa Telegram wanda shi ma manhajar sakonni ne, amma ya bambanta da WhatsApp a wajen adana bayanai a duniyar gizo da kuma bai wa masu amfani da shi daman bude dandali mai daukan mambobi 200,000.


Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "WhatsApp zai fito da tsarin samun taska daya a wayoyi daban"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Barka Da Zuwa Duniyar Sadarwa!

Manufar Duniyar Sadarwa shi ne ilimantarwa da wayar da kan al'ummar Hausawa a game da al'amuran fasaha da kere-keren zamani.

Mun dawo da tsofaffin kasidun da muka wallafa tun a tsohon shafin mu na MyWapBlog zuwa wannan sabon shafin wanda a yanzu yake kan manhajar ZamaniWeb.


Kasidu Masu Alaka