Duniyar Sadarwa

Sababbin al'amuran fasahar sadarwan zamani, shawarwari da bayanan yadda ake... a harshen Hausa!

Netflix Ya fara bada daman kallon wasu fina-finai kyauta, a boye

Wallafan October 10, 2020. 2:34pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Labaran Fasaha

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/10/1/netflix-03-1.jpg

Manhajar kallon fina-finai ta intanet mafi shahara wato Netflix ya fara bayar da daman kallon wasu fina-finai a kyauta amma cikin sirri. Fina-finan sun hada da drama da wasannin kwaikwayo masu dogon zango da wasannin yara har ma da wasu shirye-shirye na musamman.

Ana ganin wannan na cikin tsarin da Netflix ke kokarin fitowa da shi wanda zai bai wa mutane daman kallon zangon farko na wasu shahararrun fina-finai masu dogon zango har ma da wasu cikakkun fina-finai a kyauta, ba tare da sai sun yi rajista ko sun shiga tsarin biyan kudi ba.

A halin yanzu ana iya riskan fina-finan na kyauta ne ta bayan fage a shafin Netflix din ta hanyar amfani da wayar Android ko kuma kwamfuta, amma ba a iya samun shiga ta wayoyin iPhone. Kuma shafin na 'Kallo kyauta' ba a samun shi daga shafin farko na Netflix din kai-tsaye har sai an bi ta shafin 'help desk'.

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/10/1/netflix-kallo-kyauta.png

Kawo yanzu dai, Netflix bai fitar da wani sanarwa a kan hakan ba. Sai dai wasu na ganin cewan kamfanin yana yin gwajin wannan tsarin ne kafin daga bisani ya sanya shi cikin tsare-tsaren sa, idan ya ga akwai riba a sakamakon hakan.

Duk da kasancewan Netflix manhajar kallon bidiyo ta intanet mafi shahara, ya kasance a kodayashe mai kokarin bullo da sabbin dabarun samun karin masu amfani da manhajar. Baya ga labari irin wannan ma, akwai kuma wani labarin da ke nuna cewan kamfanin na kokarin yin hadin gwiwa da masana'antun shirya fina-finai na kasashe daban-daban. Inda ko a watan Augustan shekarar 2019 ya fara haska fim din sa na farko, wanda fim ne na 'yan kasar Malesiya mai taken The Ghost Bride wanda kuma ya saki a watan Janerun wannan shekarar ta 2020.

A watan Maris din da ta gabata kuma, an ruwaito cewan Netflix din ya samu karin yawaitar masu amfani da shi a sakamakon yaduwar annobar cutar korona a fadin duniya. Inda ya samu masu shiga tsare-tsaren sa har kusan miliyan 15 a watan Afrilun da ta gabata. Sai dai ana ganin kamfanin zai iya samun cikas wajen tabbatar da dorewar biyan bukatun masu tururuwan amfani da shi din bayan annobar ta kare.


Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Netflix Ya fara bada daman kallon wasu fina-finai kyauta, a boye"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Barka Da Zuwa Duniyar Sadarwa!

Manufar Duniyar Sadarwa shi ne ilimantarwa da wayar da kan al'ummar Hausawa a game da al'amuran fasaha da kere-keren zamani.

Mun dawo da tsofaffin kasidun da muka wallafa tun a tsohon shafin mu na MyWapBlog zuwa wannan sabon shafin wanda a yanzu yake kan manhajar ZamaniWeb.


Kasidu Masu Alaka