Duniyar Sadarwa

Sababbin al'amuran fasahar sadarwan zamani, shawarwari da bayanan yadda ake... a harshen Hausa!

Kamfanin Stripe ya sayi kamfanin PayStack a Najeriya

Wallafan October 23, 2020. 9:18am. Na Ahmad Bala. A Sashin Labaran Fasaha

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/10/1/haduwan-cinikin-stripe-da-paystack.png

A satin da ta gabata ne wani shahararren kamfanin biyan kudi ta intanet mai suna Stripe daga kasar Amurka ya sayi kamfanin PayStack na Najeriya a kan kudi sama da dalar Amurka miliyan 200. PayStack dai shi ne kamfanin biyan kudi ta intanet mafi shahara a Najeriya wanda a halin yanzu mutanen da ke amfani da shi a Najeriyar da kuma kasar Gana sun zarce 60,000. Inda a halin yanzu kuma kamfanin ke kokarin fadada harkokin sa zuwa sauran kasashen Afrika.

Kawo yanzu dai, wannan shi ne cinikin kamfanin intanet mafi girma da aka taba yi a Najeriya. Kuma karo na farko da wani kamfanin intanet daga Amurka ya saye kamfanin intanet a Najeriya.

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/10/1/paystack-co-founders.jpg

Shola Akinlade shi ne ya kirkiro kamfanin na PayStack a shekarar 2015, tare da wani abokin sa mai suna Ezra Olubi. Domin kawo mafita kan matsalar biyan kudi ta intanet da akan fuskanta a Najeriya. PayStack manahajar yanargizo ne da ke bada daman biyan kudi a intanet ta hanyoyi mabambanta wanda suka hada da hanyar katin banki wato 'credit card' da 'debit card' da kuma biya ta bankin intanet ga masu saye da sayarwa a shafukan yanargizo da kuma manhajojin wayar hannu.

A shekarar 2018 ne kamfanin na PayStack ya samu tururuwan masu zuba hannun jari inda ya tara dala miliyan 8 daga wasu manyan kamfanoni da 'yan kasuwa daga sassa daban-daban na duniya, wandanda ke yi wa PayStack din kallon sabon fasahar da zai iya samar da kyakkyawar riba a nan gaba.

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/10/1/stripe-ya-saye-paystack-a-najeriya.png

Kamfanin na PayStack ya bayyana cewan zai ci gaba da gudanar da harkokin sa tare da sunan da aka san sa da shi, kuma a matsayin sa na kamfani mai cin gashin kan sa duk da kasancewar sa mallakin Stripe din a yanzu.


Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Kamfanin Stripe ya sayi kamfanin PayStack a Najeriya"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Barka Da Zuwa Duniyar Sadarwa!

Manufar Duniyar Sadarwa shi ne ilimantarwa da wayar da kan al'ummar Hausawa a game da al'amuran fasaha da kere-keren zamani.

Mun dawo da tsofaffin kasidun da muka wallafa tun a tsohon shafin mu na MyWapBlog zuwa wannan sabon shafin wanda a yanzu yake kan manhajar ZamaniWeb.


Kasidu Masu Alaka