Duniyar Sadarwa

Sababbin al'amuran fasahar sadarwan zamani, shawarwari da bayanan yadda ake... a harshen Hausa!

Kamfanin Facebook zai bude sabon ofishi a Najeriya

Wallafan October 9, 2020. 1:21am. Na Ahmad Bala. A Sashin Labaran Fasaha

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/10/1/markzurk-in-lagos.png

Kamfanin Facebook ya sanar da fara shirye-shiryen kaddamar da sabon ofishin sa a birnin Legas a Najeriya. Ofishin shi ne zai kasance na biyu a Afrika, inda ofishin Facebook din na kasar Afrika ta kudu ya kasance na farko. Wannan labari na zuwa ne bayan shekaru hudu da kawo ziyarar shugaban kamfanin Mark Zurkerberg zuwa kasar ta Najeriya.

Zuwan Facebook Najeriya dai abu ne da ake ganin zai bayar da gagarumar gudun mawa wajen ci gaban harkokin fasaha a kasashen yammacin Afrika. Ana hasashen cewan sabon ofishin na Facebook zai fara aiki ne a tsakiyar shekara mai zuwa na 2021.

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/10/1/facebook-office-780x405.jpg

Kididdaga a Najeriyar dai na nuni da cewan kimanin mutane miliyan 33 ke amfani da manahajar Facebook din a kowane wata. Inda kimanin 'yan kasar miliyan 16 kuma ke amfani da shi a kullum. Wanda hakan ne ya sa Najeriyar ta kasance kasa ta daya wacce ta fi kawo wa kamfanin na Facebook kudaden shiga a Afrika baki daya.


Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Kamfanin Facebook zai bude sabon ofishi a Najeriya"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Barka Da Zuwa Duniyar Sadarwa!

Manufar Duniyar Sadarwa shi ne ilimantarwa da wayar da kan al'ummar Hausawa a game da al'amuran fasaha da kere-keren zamani.

Mun dawo da tsofaffin kasidun da muka wallafa tun a tsohon shafin mu na MyWapBlog zuwa wannan sabon shafin wanda a yanzu yake kan manhajar ZamaniWeb.


Kasidu Masu Alaka