Duniyar Sadarwa

Sababbin al'amuran fasahar sadarwan zamani, shawarwari da bayanan yadda ake... a harshen Hausa!

Gwamnatin kasar Uganda ta kara tsaurara dokoki a kan masu wallafa bayanai a yanargizo

Wallafan October 19, 2020. 9:12pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Labaran Fasaha

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/10/1/shafukan-sadarwan-intanet-a-uganda.png

Gwamnatin kasar Uganda ta kara tsaurara dokoki ga 'yan kasar masu wallafa bayanai a shafukan sada zumunta irin su Facebook da Youtube, har ma da sauran mawallafa a yanargizo wato bloggers. A bisa wata sabuwar dokar da gwamnatin ta bullo da shi, dole ne sai kowane dan kasa ya yi rajista tare da mallakar lasisi daga hukumar sadarwa ta kasar wato Ugandan Communications Commission (UCC) kafin ya wallafa duk wani bayani a kafafen sadarwa.

A bisa sanarwan da hukumar ta fitar, dokar ta fara aiki ne daga ranar 5 ga watan Oktoban wannan shekara ta 2020. Kuma dokar ta shafi dukkanin mawallafa ne a kafafen sadarwa. Har da masu wallafa shirye-shiryen sauraro a yanargizo da gidajen rediyo da talabijin da tashoshin Youtube da kuma shafukan blog.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da gwamnatin kasar ta Uganda ke sanya irin wannan dokoki ga masu wallafa bayanai ta yanargizo a kasar ba. Sai dai duk da irin wadannan dokoki, alkalumman kididdiga na Alexa Rank na nuni da cewan shafukan Google da YouTube da kuma Facebook su ne shafukan yanargizo da ke samun mafi yawan maziyarta a kasar. A bisa kididdigan DataReportal, masu amfani da shafukan sada zumunta a yanargizo sun kai miliyan 2.5 inda daukacin masu amfani da intanet su kuma suka kai miliyan 10.2 a kasar ta Uganda.

Wani darakta na kungiyar kare hakkin dan adam na Amnesty International mai suna Deprose Muchena ya bayyana wannan sabuwar doka a matsayin tauye 'yancin bayyana ra'ayi da kuma dakile hanyoyin samun bayanai a yayin da zaben kasar ta Uganda na 2021 ke kara kusantowa.


Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Gwamnatin kasar Uganda ta kara tsaurara dokoki a kan masu wallafa bayanai a yanargizo"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Barka Da Zuwa Duniyar Sadarwa!

Manufar Duniyar Sadarwa shi ne ilimantarwa da wayar da kan al'ummar Hausawa a game da al'amuran fasaha da kere-keren zamani.

Mun dawo da tsofaffin kasidun da muka wallafa tun a tsohon shafin mu na MyWapBlog zuwa wannan sabon shafin wanda a yanzu yake kan manhajar ZamaniWeb.


Kasidu Masu Alaka