Duniyar Sadarwa

Sababbin al'amuran fasahar sadarwan zamani, shawarwari da bayanan yadda ake... a harshen Hausa!

Cruise ya samu lasisin fara gwajin mota maras matuki a birnin San Francisco

Wallafan October 29, 2020. 1:18pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Labaran Fasaha

Kamfanin da ke kera motocin zamani marasa matuki mai suna Cruise ya samu lasisin fara yin gwajin motocin sa a titunan birnin San Francisco na jihar Carlifornia a Amurka. Wannan ne karon farko da hukumar kula da harkokin gwaje-gwajen ababen hawa a kasar ta amince wa kamfanin na Cruise yin gwajin motocin sa har guda biyar a wasu manyan titunan birnin.

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/10/1/mota-maras-matuki-na-cruise.jpg

Tun a shekarar 2015 kamfanin Cruise ya samu wani lasisin fara gudanar da gwaje-gwajen motocin sa marasa matuki a birnin na San Francisco wanda ake yi wa kallon daya daga cikin biranen da ke da wahalan tuki a duniya. Sai dai a wancan lokacin, lasisin takaitacce ne, domin kuwa dole ne sai an sanya wani matuki ya zauna a cikin motar domin kula da yadda motar ke tuka kan ta, don gudun hatsarin da ka iya faruwa sanadiyar tangardan na'ura. Amma a wannan karon, kamfanin ya samu cikakken lasisin da ya ba shi daman yin gwajin motocin ba tare da sanya wani mutum a ciki ba.

"Ba mu ne kamfani na farko da ya fara samun wannan lasisin ba. Amma a yanzu za mu kasance na farko wanda suka fara yin gwajin a daya daga cikin manyan biranen Amurka. Kafin karshen wannan shekarar za mu fara dora motocin mu a kan titunan San Francisco, su rika tafiya ba tare da amfani da man fetur ba, kuma ba tare da wani dan'adam a cikin su ba." in ji shugaban kamfanin na Cruise, Dan Ammann.

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/10/1/motar_cruise.jpg

Wannan dai wani babban matakin nasara ne ga kamfanin na Cruise wanda ya shafe tsawon shekaru shida yana aikin kera wadannan motoci masu aiki da wutan lantarki, wanda ba su bukatar mai tuki.


Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Cruise ya samu lasisin fara gwajin mota maras matuki a birnin San Francisco"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Barka Da Zuwa Duniyar Sadarwa!

Manufar Duniyar Sadarwa shi ne ilimantarwa da wayar da kan al'ummar Hausawa a game da al'amuran fasaha da kere-keren zamani.

Mun dawo da tsofaffin kasidun da muka wallafa tun a tsohon shafin mu na MyWapBlog zuwa wannan sabon shafin wanda a yanzu yake kan manhajar ZamaniWeb.


Kasidu Masu Alaka