Duniyar Sadarwa

Sababbin al'amuran fasahar sadarwan zamani, shawarwari da bayanan yadda ake... a harshen Hausa!

An Hana Donald Trump Yin Amfani Da Facebook, Instagram Da Twitter

Wallafan January 10, 2021. 2:23pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Labaran Fasaha

http://zamaniweb.com/administrator/files/21/01/1/donald-trump-twitter.png

A satin da ya gabata ne kamfanin Facebook ya dakatar da shugaban Amurka Donald Trump daga ci gaba da amfani da manhajoin sa na Facebook da Instagram. Hakan ya biyo bayan tarzomar da ya faru a majalisar dokokin kasar da ke birnin Washinton DC. Inda magoya bayan Donald Trump suka kutsa cikin ginin majalisar, lamarin da yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane 5 da raunata wasu da dama, a ranar larabar da ta gabata.

Shugaban kamfanin na Facebook, Mark Zuckerberg, ya baiyana cewa taskan Facebook da Instagram na Donald Trump zai ci gaba da kasancewa a kulle har zuwa ranar 20 ga wannan wata na Janeru, wato ranar da za a rantsar da sabon shugaba, Joe Beiden kan kujerar shugabancin kasar.

Zuckerberg ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafin sa na facebook, inda ya kara da cewa: "Muna da yakinin cewa barin shugaba Donald Trump ya ci gaba da amfani da manhajojin mu a wannan lokacin hatsari ne babba".

http://zamaniweb.com/administrator/files/21/01/1/facebook-mark-zuck-ya-rufe-shafin-donald-trump.png

Ya kuma ce sun dauki wannan matakin ne domin shugaba Donald Trump ya yi amfani da Facebook din wajen rura wutar "tayar da tarzoma a kan wanda ya lashe zabe a demokradiyyance".

Biyo bayan wannan ne kuma, sai shi ma kamfanin Twitter karkashin jagorancin Jack Dorsey ya rufe shafin twitter na Donald Trump din baki daya. Twitter ya ce ya rufe shafin twitter na shugaban ne mai taken @realDonaldTrump bayan bibiyan abubuwan da ya wallafa a shafin nasa a 'yan kwanakin nan, domin kauce wa hatsarin "ci gaba da rura wutar tayar da tarzoma".

http://zamaniweb.com/administrator/files/21/01/1/twitter-ya-rufe-shafin-donald-trump.png

Kamfanin na twitter ya yi karin bayani game da matakin rufe shafin shugaban a wani rubutun da ya wallafa na musamman a shafin sa na blog


Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "An Hana Donald Trump Yin Amfani Da Facebook, Instagram Da Twitter"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Barka Da Zuwa Duniyar Sadarwa!

Manufar Duniyar Sadarwa shi ne ilimantarwa da wayar da kan al'ummar Hausawa a game da al'amuran fasaha da kere-keren zamani.

Mun dawo da tsofaffin kasidun da muka wallafa tun a tsohon shafin mu na MyWapBlog zuwa wannan sabon shafin wanda a yanzu yake kan manhajar ZamaniWeb.


Kasidu Masu Alaka